Kasar Sin za ta samar da rancen kudi mai rangwamen ruwa domin taimakawa shirin samar da tsarin sadarwar yanar gizo a kasar Angola.
An samar da shirin ne karkashin yarjejeniyar rance mai rangawame da aka rattabawa hannu jiya a Laraba.
Yarjejeniyar ta kasance a karkashin bankin kula da harkokin shige da ficen kayayyaki na kasar China, a matsayin wanda zai samar da kudin da ya kai dala biliyan 249, domin shimfida hanyar sadarwar intanet mai tsawon kilomita 2,000 da za ta bi karkashin kasa da kuma wadda za ta hada kasar da yankin Cabinda da ruwa ya ratsa tsakaninsu, tare da inganta baki dayan tsarin sadarwa na kasar Angola.