Yau Laraba, ministan harkokin wajen kasar China Qin Gang, ya gana da shugaban kwamitin kungiyar AU Musa Faki Muhammad domin gudanar da shawarwari bisa manyan tsare-tsare karo na takwas tsakanin Sin da AU a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
A yayin shawarwarin, Qin Gang ya ce, a ko da yaushe kasar Sin tana dora Afirka a matsayin mai fifiko a harkokin diflomasiyyarta, kuma gado, da ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka gaba ya zama al’ada mai daraja, kana wani muhimmin tarihi na diflomasiyyar kasar China.
Muna son ci gaba da zama abokan huldar ci gaba tare da Afirka don samun ci gaba tare, da hada karfi don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani. A cewarsa, kasar Sin ce ke kan gaba wajen tallafawa kungiyar AU ta shiga G20, da goyon bayan inganta wakilci da muryar kasashen Afirka a kwamitin sulhu na MDD, da sauran kungiyoyin kasa da kasa, da kuma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.
A nasa bangaren, Faki ya bayyana cewa, Sin na goyon bayan Afirka, a yayin da jama’ar Afirka ke gwagwarmayar neman ‘yancin kai da ‘yantar da al’umma, da ma kokarin da kasashen Afirka ke yi na hanzarta samun bunkasuwa, da farfadowa, da kuma shiga cikin harkokin kasa da kasa.
Ya kara da cewa, “muna mutunta babban goyon bayan da kasar Sin ke bayarwa ga dunkulewar kasashen Afirka, da cudanya, da gina yankin ciniki cikin ‘yanci, muna kuma fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani”.
Bayan shawarwarin, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan wasu takardun hadin gwiwa, ciki har da yarjejeniyar tattalin arziki, da fasaha kan cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka, tare da halartar bikin kammala ginin hedkwatar cibiyar