• About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
No Result
View All Result
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
Home HAUSA NEWS

A cikin shekara 14 na haifi “ya”ya 18

B. IMAM by B. IMAM
October 11, 2022
in HAUSA NEWS
0
0
SHARES
Share on FacebookShare on Twitter

Wasu mutane a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun fara kiran wata mata mai suna Hajara Shu’aibu da cewa ita ce mace mafi haihuwa a kasar saboda yawan ‘ya’yan da ta haifa inda ta haifi ‘yan biyar a baya-bayan nan.

Matar ta haifi tagwaye sau biyu sannan ta haifi dai-dai sau tara sannan kuma a yanzu ta haifi ‘yan biyar, jumulla ‘ya’ya 18 kenan.

RelatedPosts

China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO

China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO

March 25, 2023
Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

March 25, 2023

APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa

March 24, 2023

A tattaunawarta da manema labarai kan haihuwar da ta yi ta ‘yan-biyar a karshen nan ta ce babu wani sauyi da ta ji ko tsammanin cewa za ta haifi abin da ya fice da daya.

Ta ce ko awon ciki ba ta taba zuwa ba, haka ta haife su a gida da taimakon ungozoma, inda bayan ta sauka ne sai aka tafi da su babban asibitin Funtua domin a duba lafiyarta da jariran.

Zuwansu asibitin ne ta ce, sai aka kara mata jini aka ce, mata ta samu ta huta, tana mai karin bayani da cewa dukkanin sauran haihuwar da ta yi a baya ba ta taba zuwa asibiti ba a gida ta yi, kuma ba tare da an yi mata tiyata ba.

Hajara wadda ta ce ita matar aure ce da ke zaman gida kawai ba wani aiki ko sana’a da take yi, ta ce ba wani abinci na daban ko wani abu na daban da take yi da ke sa ta haihuwa da yawa irin wannan.

Ta ce, ”Ikon Allah ne kawai, ba wani abu nake ci ba na musamman da ke sa ni haihuwa da yawa.”

Matar ta yi roko ga gwamnati da sauran jama’a da su taimaka musu kan yadda za su kula da ‘ya’yan.

Sai dai kuma mijin wannan mata wato mahaifin wadannan jarirai Shu’aibu Umar ya gaya wa manema labarai cewa biyu daga cikin jariran sun rasu washegari bayan haihuwarsu ranar Laraba.

Amma ragowar ukun suna nan da ransu, sai dai an kai su Babban Asibitin Tarayya na Katsina tare da mahaifiyar domin kula da su yadda ya kamata.

Ya ce a babban asibitin na Funtua babu kwalba da za a sa jariran saboda haka ne aka tura su zuwa cibiyar gwamnatin tarayyar ta Katsina inda yanzu suke samun kulawar da suke bukata.

Shu’aibu wanda manomi ne a kauyen Doma na jihar ta Katsina ya ce, ya dauki ‘ya’ya a matsayin wata baiwa da rahama daga Allah.

Amma ba wani abinci na musamman da matarsa take ci ko wani abu da take yi da ke sa tana haihuwa da yawa haka.

Mutumin ya ce shugaban karamar hukumar Faskari a jihar ta Katsina ya taimaka musu da Naira dubu 100, amma har yanzu suna bukatar taimako domin kula da iyalin.

Mijin matar, Shuaibu Umar, ya ce suna bukatar taimakon kula da yaran

Umar Hussaini wanda shi ne mahaifin Hajara ya ce ya aurar da ‘yar tasa tun shekara 21 da ta gabata.

Ya ce “Shekarar Hajara 35 kuma ta yi aure tun shekara 21 da ta gabata, a dangane da yawan haihuwarta sai in ce wata baiwa ce daga Allah.’’

An tambayi mahaifiyar jariran Hajara ko za ta sake haihuwa nan gaba “sai ta ce lamarin ba a hannunta yake ba, Allah ne Yake da komai Idan Ya kaddara zan sake haihuwa zan haihu.

Tags: AHMAD MUSAALAN WAKAALI JITAALJAZEERAALKIBULAALKUKIArewaAREWA24banditBBCBOOLWOODBUK RADIOCNNdailytrustDALA RADIOFACEBOOKFIFAGARBA SHEHUHAUSA7HEALTHIZZAR SOJALLAKADAURA24KAKAKIKANNYWOODKano pillarsLABARAI 24LIBERTY RADIOMADAGWALMC TAGWAYEMESSIPLAYSTORPREMIER LIGUERPREMIER RADIOPYRAMID RADIORANA 24RARARARIFRONALDOSAUDIPRESSSOLESEBASETWEETERVANGUARDVISION RADIOWHATAPP
ShareTweetSendSharePin
Previous Post

Karamar hukumar bebeji ta amsa kiran dan ta

Next Post

Da mutane zasu kyautata mu’amalar su da yanuwan su da sun Sami saukin bala’o’in da suka addabe su: Sheikh Ibn Sina

B. IMAM

B. IMAM

RelatedPosts

China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO
HAUSA NEWS

China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO

by Aksam Media
March 25, 2023
0

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce kafin Amurka ta koma cikin hukumar raya...

Read more
Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

March 25, 2023
APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa

APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa

March 24, 2023
CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma

CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma

March 24, 2023
Matashi mai tattaki daga Garin Kubau zuwa Kaduna dan taya murna ga,  sen Uba Sani, tafiya ta nisa

Matashi mai tattaki daga Garin Kubau zuwa Kaduna dan taya murna ga, sen Uba Sani, tafiya ta nisa

March 24, 2023
Abubuwan da cin su ke hana shan wahalar Azumi komai rana

Abubuwan da cin su ke hana shan wahalar Azumi komai rana

March 24, 2023
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Login
Notify of
guest
guest
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

March 10, 2023
Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

February 21, 2023
Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

February 11, 2023
INEC tayi umarnin kara gudanar da zabe a jihar Kogi

Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

March 19, 2023
CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

2
Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

1
Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

1
Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

1
China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO

China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO

March 25, 2023
Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

March 25, 2023
APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa

APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa

March 24, 2023
CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma

CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma

March 24, 2023
  • Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yanzu-yanzu an kama wani Dan Majalisa dauke da makuden kudaden waje

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO
HAUSA NEWS

China ta soki kasar Amurka bayan da ta shiga UNESCO

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce kafin Amurka ta koma cikin hukumar raya ...

March 25, 2023
Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu
HAUSA NEWS

Ada na sha ruwan kwata sabo da Buhari da jam’iyar sa amma yanzu Ina Allah wadai da ita: Matashi Aliyu

Aliyu Muhammad ya tsallake rijiya da baya a 2019, saboda makauniyar soyayya daya samu kansa a ciki ta Shugaba Muhammadu ...

March 25, 2023
APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa
HAUSA NEWS

APC ta musanta ganawa tsakanin Tinibu da alkalin alkalai na kasa

Kwamatin yakin neman zaben na Dan takarar jam’iyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinibu ya musanta raderadin da wasu kafafen sadarwa ...

March 24, 2023
CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma
HAUSA NEWS

CBN ya soma gudanar da rangadi domin hukunta Bankuna da basa bayar da tsofaffin takardun kuɗi ga alumma

Daga kabiru A Dukawa Babban bankin Najeriya CBN ya ci alwashin hukunta duk wani bankin yan kasuwa da ya samu ...

March 24, 2023
Matashi mai tattaki daga Garin Kubau zuwa Kaduna dan taya murna ga,  sen Uba Sani, tafiya ta nisa
HAUSA NEWS

Matashi mai tattaki daga Garin Kubau zuwa Kaduna dan taya murna ga, sen Uba Sani, tafiya ta nisa

Matashi mai suna Yusuf Umar ya ga dacewar zuwa Kaduna garin gwamna ne domin taya sabon zababben gwamnan jihar Kaduna ...

March 24, 2023

Recent Comments

  • Ibrahim S kabara on Hukumar kula da ayyukan yan sanda ta raba lambobin kiran waya Dan sa Ido a ayyukan yan sanda a lokacin zabe
  • Abbas Jibril on Katu ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya
  • Walid Y Haris on Akwai Malaman cocin dake kallan batsa a yanar gizo ta wayoyinsu-Fafaroma
  • Abba Garba Sufi on Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.
  • Sani saadu aliyu on CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

wpDiscuz