Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya iso zauren majalisar tarayya kuma an fara zaman majalisa yayin da yan Najeriya ke jiran jerin sunayen ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sabuwar doka da aka yi a Najeriya ta ba wa shugaban kasa kwana 60 ya fitar da ministocinsa kuma wannan wa’adin zai cika zuwa karshen wannan makon.
Akpabio ya isa majalisa tun misalin kargfe 12.10 na rana sannan ya shiga zauren don fara zama na musamman.
Ana sa ran shugaban majalisar zai karanta jerin sunayen ministocin na Shugaba Tinubu a yau, Alhamis, 27 ga watan Yuli, yayin zaman majalisar.
Akwai alamun cewa a halin yanzu an kawo sunayen ministocin majalisar ta tarayya.
Tinubu, wanda ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023, yana da kwana 60 bisa kundin tsarin kasa ya fitar da ministocinsa.