Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraran karar da aka shigar akan tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami kan zargin karfa-karfa.
Kotun, ta bakin Alkalinta, Oluyemisi Adelaja ya dage sauraran karar zuwa 17 ga watan Oktoba don ba wa wanda ake karar daman shiryawa, Legit.ng ta tattaro
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa wani dan kasuwa, mai suna Cecil Osakwe shi ya maka tsohon ministan a gaban kotun.
Zargin da ake yi wa Abubakar Malami A cikin karar, da dan kasuwar wanda dillalin filaye ne a Abuja ya ce Malami ya tilasta masa ba wa wata ma’aikaciyar gwamnati, mai suna Asabe Waziri gidaje biyu a Maitama.
Ya kuma ce Malami ya tilasta masa ba wa Waziri kadarar da ta kai kimar miliyan 130 kuma ya ce Malami ya shiga tsakani a matsalar kamfaninsa da Asabe Waziri.
Ya kara da cewa Malami ya umarci jami’an tsaronsa su ci gaba da cin zarafinsa lokacin da ya ke minista. Ya ce da sanin Malami Waziri ta shafe watanni takwas a gidan kafin kotu ta fitar da ita.