Yayin da tsadar man fetur ke kara jawo matsala a Najeriya, gwamnatin Edo ta samo mafita ga fannin ilimi a firamare da karamar sakandare
Yanzu haka, za a fara karatun kwanaki uku a mako a madadin biyar da aka saba dashi a cikin makon karatu.
Hakazalika, ma’aikatan gwamnati za su fara batun rage kwanakin aiki don rage radadin tafiyar da aiki a jihar
An zabi ranakun Litinin, Talata da Laraba a matsayin ranakun da yaranmu za su je makaranta yayin da za a rufe makarantu a ranakun Alhamis da Juma’a.
Tsarinmu na wannan lokacin ya mayar da hankali ne kan habaka karatu ta yanar gizo don tabbatar da cewa yaran sun kammala tsarin darussan da ya kamata su dauka.
“Za su zauna a haka na tsawon makwanni shida kafin hutu. Bisa la’akari da dalilai na gudanarwa, mun zabi kwanaki uku na farkon mako domin dalibai su zo makaranta.
“Mun kara sa’o’in karatun firamare a fadin jihar da sa’a daya sai kuma sa’o’i biyu ga kananan makarantun sakandare domin cimma tsarin darussan tare da sanya jadawalin ranakun Alhamis da Juma’a zuwa ranakun Litinin, Talata da Laraba