Kungiyar kasuwar masu sana,ar magunguna ta jihar kano,dake malam kato ta yi kira ga alummar Najeriya, da su kwantar da hankulansu sakamakon tashin gwauran zabi da man fetur yayi saboda cire tallafin mai da Gwamnatin tarayya tayi.
Shugaban kula da alamuran da suka shafi matasa, Alh mamuda zangon kabo ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishisa dake kasuwar.
Mamuda zangon kabo yace,kamata yayi alummar Najeriya su ci gaba da gudanar da addu,oin samun sauki daga wajen Allah subahanahu wata,ala,kasancewar itace,kawai mafita ga yannajeriya .
Ya kuma, bukaci Gwamnatin tarayya da ta tausayawa alummar kasar nan, musamman wadanda basu da hali,kuma ba ma,aikatan Gwamnati bane,duk da cewa Gwamnatin tarayya tana cewa za ta karawa ma,aikatanta Albashi.
Shugaban ya bayyana cewa, su Kansu alummar Najeriya abin a duba lamarin sune saboda halin matsin rayuwa da za su tsinci kansu, da yawa wasu daga cikin alumma sai sun fita za su samu abin da za su ciyar da iyalansu wadanda akasari sune suka ci yawa a fadin kasar nan.
Mamuda yace,akwai kananan yankasuwa da suke karancin jari da za su gudanar da sana,oinsu na yau da kullum,Amma cire tallafin da Gwamnatin tarayya tayi,ya kara durkusar da su,sakamakon tashin kayayyakin masarufi,duba da man fetur yana tafiya kowanne fannin na rayuwar alummar Najeriya.
Haka zalika,zangon kabo,ya shawarci masu kananan sana,oi da yankasuwa da su kasance masu yin lissafi a kasuwancinsu na yau da kullum domin fahintar yadda kasuwancinsu yake tafiya, Wanda yin hakan zai taimaka musu wajen sanin inda suka dosa.
Daga karshe ya shawarci kungiyoyin yankasuwa da manyan yankasuwa da su kasance masu tallafawa kananan yankasuwa da suke da karancin jari domin tallafa musu a harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.
Ibrahim sani gama pyramid radio.