kasar China tana adawa da yin katsalandan a cikin harkokin cikin gidan kasashen dake tasowa, bisa hujjar kare hakkokin bil’adama.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wen bin ne, ya bayyana inda yace matakin da China ya samu goyon-baya daga wasu o, musamman ma kasashe masu tasowa.
Wang ya yi wannan furucin ne, yayin da yake gabatar da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya sha’anin kare hakkokin dan Adam. Ya ce tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kwamitin kolin jam’iyyar dake karkashin shugabancin Xi Jinping, yana maida aikin girmamawa, gami da kare hakkokin dan Adam a matsayin wani muhimmin aiki na mulkin kasa, don samar da ci gaba ga sha’anin kare hakkokin dan Adam na kasar Sin.
Wang ya kara da cewa, kasarsa na nuna kwazo, wajen halartar ayyukan kare hakkokin dan Adam na duk duniya, kuma har sau uku kwamitin kula da hakkokin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kudirin da kasar Sin ta gabatar, dangane da gudummawar da ci gaba ya bayar, ga more dukkanin hakkokin dan Adam, gami da fadada hadin-gwiwa a fannin hakkokin dan Adam. Hakan na nufin ra’ayoyin kare hakkokin dan Adam ta hanyar samar da ci gaba, da fadada hadin-gwiwa ya shiga zukatan al’ummomin kasa da kasa.
Wang ya ce, kasar Sin tana son yin kokari tare da bangarorin kasa da kasa, domin samar da ci gaba ga hakkokin dan Adam na duniya, da kara kirkiro makoma mai haske.