Bankin ‘Finance Trust’ da ke aiki a kasar, Uganda ya sanar da cewa yanzu haka ya kaddamar da “asusun bankin halal” a matsayin wani reshen bankin.
Shugaban sashin hada-hadar Kasuwanci na bankin Percy Lubega, shine ya sanar da hakan ga manema labarai
Lubega ya kara da cewa ta haka ne Musulman kasar za su iya karban bashi daga bankin ba tare da biyan riba ba, ya kuma tunatar da cewa an bude asusun bankin bisa tsarin addinin Musulunci a karon farko a kasar Uganda.
Wani dan kasuwa dan kasar Uganda, Hahh Karim Kallisa, a cikin tantancewar da ya yi kan wannan batu, ya ja hankali da cewa wannan asusun bankin halal mataki ne mai fa’ida ba ga Musulmai kadai ba, har ma ga dukkan makiya addinin musulunci .