Bayan Kurewar Lokaci CBN ya sake fitar da wani Sabon tsarin canza kudade a banki
Babban bankin Najeriya ya bayyana bullo da sabon shiri na shigar da tsoffin kudaden 1000, da 500, da kuma 200 biyu cikin bankuna.
CBN ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da Haruna Mustafa, Daractan bangaren sa Ido da Musa I. Jimoh, Daractan bangaren shigar da kudaden bankuna suka saka was hanu a jiya Asabar.
CBN ya bayyana bullo da tsarin mai cike da Kalu bale ga mutanen karkara ne a jiya Asabar inda yace zai fara aiki daga ranar Litinin
A cewar sa kowanna mutum zai sami damar canza tsoffin kudaden sa ne kawai dazarar ya bude Asusun Banki ko kuma maajiyar walet.
Kazalika yace idan hakan bata samu ba kadai mutum zai sami canjin Naira 10,000 ne kadai a hanun sa abin da ya rage masa kuwa sai dai su kasance a Asusun sa.
Shirin canza kudi mai suna ” Naira redesign policy” a turance an tanadi shi ne domin mutanen karkara a cewar CBN