China ta yi hasashen kara bunkasa tattalin arzikin ta a 2023

Bisa la’akari da sauya dabaru da matakan kandagarkin cutar COVID-19 da wasu dabarun raya tattalin arziki, masu zuba jari na ketare na sa ran tattalin arzikin kasar China  zai kara farfadowa.

Kwanaki kalilan bayan shiga sabuwar shekarar 2023, kasuwannin musayar kudaden ketare da ta hannayen jari na kasar Sin sun kara karfi, haka kuma azurfa da zinare na kasashen ketare na samun karbuwa a kasar.

Bayanai na baya-bayan nan daga babban bankin kasar Sin sun bayyana cewa, tun daga karshen bara, farashin musayar takardar kudin Sin wato RMB, ya farfado sosai, haka kuma jarin waje na ci gaba da karuwa a kasar, wadanda ke alamta cewa, kasuwar hada-hadar kudi ta ketare na da kwarin gwiwa kan tubalin tattalin arzikin kasar, kamar farashin kayayyaki.

Cikin matsakaici da dogon zango, farashin takadar kudin RMB zai ci gaba da sauyawa, kuma zai ci gaba da karfafa, lamarin dake alamta  fusknatar kalubale, ga takardar kudin RMB ta kara juriya kuma kasuwar musayar kudaden ketare ta kasar Sin na gudana yadda ya kamata, wanda ke samar da kyakkyawan yanayin habakar tattalin

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments