Kasar Uganda ta sami nasarar shawo kan annobar cutar Ebola da ta barke a kasar tun a watan Satumbar shekarar da ta gabata ta miladiya.
Ministar Lafiya ta kasar, Jane Ruth Aceng ce ta bayyana samun nasarar a wajen bukin da aka gudanar tare da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) saboda kawo karshen annobar.
Aceng ta ce an samu nasarar shawo kan annobar a kasar baki daya duda da cewa har yanzu ba a san ta kama man yadda cutar ta fara bulla ba,
Minista Aceng ta bayyana cewa an gudanar da bincike kan tushen cutar tare da abokan hulda na cikin kasar da na ketare.
Kazalika ta ce tun a ranar 19 ga watan Satumba, an samu mutane 155 da alamomin cutar, inda aka tabattar da cutar a 143 daga cikinsu, kuma mutane 55 sun mutu.
‘Tun da ba a samu bullar cutar ba cikin kwanaki 42, an dauki ranar 11 ga watan Janairu a matsayin ranar da annobar ta kawo karshe.
Cutar Ebola mai haifar da wani nau’in zazzabi mai tsanani, ta fara bayyana ne a shekarar 1976 a lokaci guda a garin Nzara da ke Sudan, da Yambuku da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.
Cutar Ebola ta bazu a yammacin Afrika a shekarar 2013 kuma ta barke a kasashen Guinea, Laberiya da Saliyo a tsakanin shekarun 2014 da 2017, mutane dubu 30 ne suka kamu da cutar, kuma sama da dubu 11 na marasa lafiya sun mutu.