Mataimakin wakilin kasar China a Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya bukaci majalisar da ta bunkasa yankin yammancin Afrika da yankin Sahel.
Bing yace yankin sun cimma muhimman nasarori wajen tabbatar da tsaro da farfado da harkokin raya tattalin arziki da zaman takewa da karfafa hadin gwiwa da goyon bayan juna, yayin da ake fuskantar yanayi mai tsanani a yankin da ma duniya baki daya.
Ya kuma ce kasar China na mara baya ga kasashen yankin tare da karfafa tsarinsu na tsaro da zurfafa tuntubar juna da hadin guiwa kan batutuwan tsaro da kafa dakarun yaki da ta’addanci na hadin guiwa da sauran dabarun tsaro da kuma kokarin inganta karfinsu na tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta’addanci.
Ya kara da cewa, kamata yayi kasa da kasa, musammam dadaddun abokan hulda, su ci gaba da taimakawa tsaron yankin da samar da karin gudunmawa ga kasashen Sahel da suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Niger, da ma sauran kasashen dake gaba-gaba wajen fama da matsalar tsaro, a fannonin samar da kudi da kayayyakin aiki da bayanan sirri da tsarin jigilar kayayyaki, domin karfafa karfinsu na yaki da ta’addanci.
Wakilin na china ya kuma nemi a mara baya ga tuntubar juna a harkokin siyasa da tattaunawa domin tabbatar da dorewar yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ya ce a bana, an shirya gudanar da zabuka a wasu kasashen yankin, don haka, Sin na fatan ’yan siyasa a kasashen za su karfafa tattaunawa da cimma daidaito da samun ci gaba a harkokin siyasa domin bada kyakkyawar gudunmawa ga ci gaban kasashensu.
Bugu da kari, ya ce a matsayinta na ’yar uwa ga kasashen Afrika, kasar Sin za ta ci gaba da ba kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel cikakken goyon baya, kuma ta shirya bayar da gudunmawa ga tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kwanciyar hankali da ci gaban yankin.