Ƙungiyar Amnesty International ta ce dole ne hukumomin Najeriya da jam’iyyun siyasar ƙasar da ‘yan takara su fito fili su yi alla-wadai da masu kalaman nuna ƙiyayya da tunzura tashin hankali da kuma razana masu zaɓe.
Ta ce ba za a lamunci yadda wasu ‘yan siyasa da idonsu ya rufe, ke ingiza tashin hankali da neman a kai wa abokan hamayya hare-hare a lokutan yaƙin neman zaɓe ba.
Amnesty na wannan kira ne, kwanaki kaɗan a fita rumfunan zabe domin kada kuri’ar zaɓen shugaban ƙasa.
Ƙungiyar ta Amnesty International ta ce gazawar hukumomi wajen gurfanar da mutanen da suka tunzara miyagun rikice-rikice a zaɓukan baya a kotu, ta haifar da wani yanayi na aikata laifi da gadara da kuma zuga wasu.
Ta ce dole ne jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da jami’an tsaro su daina lamunta ko shiga, ko tayar da hankali ko tunzara tashin hankalin da ke iya tauye ‘yancin ɗan adam.
Sanarwar ƙungiyar ta ce dole ne zaɓukan shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga wannan wata, su kasance ba tare da tarzoma ko razanarwa ba, kuma jazaman a ɓullo da matakan kare duk masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe da kuma hana keta ‘yancin bil’adama.