Hukumar kwastam ta kasar China a wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa, daga ranar 1 ga watan Maris na wannan shekara, kasar za ta soke haraji kan nau’o’in hajoji da yawansu ya kai kashi 98 cikin 100 wadanda ake shiga kasar da su daga wasu kasashen Africa.
Kasashen da garabasar ta shafa sun hada da kasar Habasha,da Burundi da kuma Jamhuriyar Nijar.
A cewar hukumar, sabon matakin zai samar da ruhin abota da hadin guiwa tsakanin China da kasashen Afirka, da taimakawa kasashe masu karamin karfi wajen bunkasa ci gabansu, da kara bude kofa ga kasashen duniya.
Sanarwar ta kara da cewa, kasar China za ta ci gaba da fadada irin wannan gatanci sannu a hankali zuwa ga dukkan kasashe mafiya karamin karfi da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin. (