Gidauniyar Malam Ibrahim Khalil dake jihar Kano ta Sha alwashin bada Gudunmowar data kamata domin ganin an Samar da shugabanci nagari a zabukan shekara ta dubu biyu da Ashirin da uku dake tafe.
Shugabar kungiyar ta jihar Kano malama Bilkisu idris Adam ce ta tabbatar da hakan a lokacin da kungiyar ta shirya taron addu,oi dangane da tafiyar siyasar malam Ibrahim khalil Wanda ya gudana a nan kano.
Malama Bilkisu tace makasudin kafa wannan kungiyar shine domin wayar da kan alumma maza da mata mahimmancin shugabanci nagari musamman wannan lokaci da alumma ta samu kanta a ciki.
Bilkisu tace kungiyar ta shirya wannan lacca ne domin wayar da kan mata akan zabar shugaba adali kuma nagari wanda zai kawo cigaba da tallafawa alumma ta fannoni da dama.
Tace lokaci yayi da mata yakamata suyi karatun ta nutsu wajen sanin wane shugaba yakamata su zaba domin ganin an samu kyakkkyawan sauyi a cikin rayuwar alumma inda yace kuma tayi Kira ga mata da suji tsoron Allah domin Allah sai ya tambayesu a ranar gobe kiyama.
Ajawabinsa Dakta Ahmed Saidu Dukawa ya ce shugabanci abune da yake da muhimmanci Wanda shine yake kawo daidaito da zaman lafiya da sanin mahimmancin Dan Adam, Wanda yayi dogon jawabi akan shugabanci da mahimmancin siyasa a rayuwar alumma .
Dukawa Ya shawarci yan kungiyar da suka shirya wannan taro da su kara zage damtse wajen Adana kuriunsu, Wanda da sune Zasu samu damar kawo sauyin shugaban da suke tunanin zai yi musu adalci.
A nata bangaren mai masaukin baki a yayin gudanar da taron uwar gidan Dan takarar Gwamna a jamiyyar ADC Hajiya Farida Ibrahim Khalil ta nuna matukar farin Cikinta bisa gudunmowa da adduoi da Gidauniyar take yiwa Malam Ibrahim khalil domin ganin an kawo sauyin shugabanci nagari a fadin jihar Kano.
Daga karshe tayi Kira ga Gidauniyar da ta cigaba da wayar da kan alumma musamman mata wajen sanin wa ya kamata su zaba domin ya zama shugabansu.