Chelsea na zawarcin Bellingham, Barcelona ta ce Messi zai dawo.
Daga Walid Hari
Chelsea ta shiga sahun masu fafutikar sayen ɗan wasan Ingila da Borussia Dortmund da ke buga tsakiya Jude Bellingham – mai shekara 19 kan £130m, Liverpool da Real Madrid duk na zawarcinsa. (Telegraph – subscription required)
Dan wasan gaba a Paris St-Germain Lionel Messi, mai shekara 35, na iya komawa Barcelona a cewar mataimakin shugaban kungiyar Eduard Romenu, wanda ya shaidawa tashar rediyon Sifaniya cewa akwai yiwuwar dawo da ɗan wasan. (The Sun)
Tottenham na son dauko mai tsaron ragar Atletico Madrid da Slovenia Jan Oblak, mai shekara 29, domin maye gurbin Hugo Lloris. (Evening Standard)
Dan wasan baya a Portugal Diogo Dalot, mai shekara 23, na fatan samun sabon kwantiragi daga Manchester United.
Everton ta shaidawa ɗan wasan Venezuela Salomon Rondon, cewa yana da damar neman wata kungiyar a Janairu, bayan gaza tafiya Turkiyya a wannan watan. (Football Insider)