Me ya sa darajar dala ke hauhawa?
Daga Walid Hari.
Dalar Amurka ta kai karfin da ba ta taba kaiwa ba a cikin shekara 20 idan aka kwatanta ta da sauran manyan kudaden duniya.
Wannan ya shafi harkokin kasuwanci da tattalin arzikin magidanta a duniya baki daya.
Kasashen da kudadensu ba su da karfi za su iya amfana da karfin dala saboda za ta sa kaya da ayyukan da suke sayar wa Amurka su yi araha, wanda hakan zai habaka cinikin da suke samu daga Amurka.
Gwamnatoci da kamfanoni a ƙasashe da dama kan karɓi bashi a dalar Amurka fiye da kuɗin ƙasarsu saboda ta fi tabbas.
A kowace shekara, ma’aikata a ƙasashen waje kan aika kuɗin da aka ƙiyasta sun kai dala biliyan 625 ga iyalansu a ƙasashensu na asali. Waɗanan kuɗaɗe za su iya yin matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasashen.
Ƙasashe da yawa a faɗin duniya na duba yadda za su haɓaka darajar kuɗaɗensu ta hanyar ƙara yawan kuɗaɗen ruwa.
Kamfanoni za su sha fama, har ma ƙila su rage ma’aikata. Iyalai kuwa za su rage kashe kuɗi.
Meye raayin ku?