Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI sun kai samame a gidansa na Mar-a-Lago da ke Palm Beach a jihar Florida.
“Kyakkyawan gidana, Mar-A-Lago da ke Palm Beach Florida a halin yanzu yana hannun gungun jami’an FBI,” in ji Trump a wata doguwar sanarwa da yammacin ranar Litinin. “Bayan bada hadin kai ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, wannan samame da aka kai gidana ba tare da sanarwa ba bai dace ba.”
Kafafen yada labarai sun ce ba a bayyana halin da ake ciki a binciken ba. Ma’aikatar Shari’a, duk da haka, tana ci gaba da bincike kan gano bayanan sirri a cikin akwatunan bayanan da aka kai gidan Trump a Florida bayan ya bar fadar White House a watan Janairun shekarar 2021.
Trump, wanda ke birnin New York a ranar Litinin, bai bayyana dalilin da ya sa jami’an suka je gidan ba. Hukumar FBI da ma’aikatar shari’a ba ta ce uffan ba nan take kan furucin na Trump.
Kakakin Ma’aikatar Shari’a Dena Iverson, ta ki cewa komai game da binciken ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press. Iverson ta kuma ki cewa komai game da ko Atoni Janar Merrick Garland ne da kansa ya ba da izinin binciken, a cewar rahotannin kafafen yada labarai.
Wani da ke da masaniya kan lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa don tattaunawa a kan binciken da ake yi, ya shaida wa AP binciken ya faru ne da safiyar Litinin.
A farkon wannan shekarar, Hukumar Kula da Tarihi ta Kasa ta ce ta gano wasu bayanan sirri a cikin akwatuna 15 a gidan Trump na Mar-a-Lago. Daga nan ta mika karar zuwa ma’aikatar shari’a.
Dokar bayanan shugaban kasa ta 1978 ta tabbatar da cewa duk bayanan shugaban kasa mallakar jama’a ne, kuma ana tura su kai tsaye a hannun ma’ajin adana kayan tarihi na kasa da zaran babban kwamanda ya bar ofis. Duk dakunan karatu na shugaban kasa da gidajen tarihi na cikin rukunin Tarihi na Kasa.