Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya nada tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban ma’aikatansa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin tarayya Abiodun Oladunjoye ya fitar.
Sanarwar tace an nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.
A ganawar da ya yi da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC a yau a Abuja, shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).
Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ya nada tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu