Gamayyar kungiyar kwadago ta kasa ta ayyana ranar Laraba mai zuwa a matsayin ranar da zata tsunduma cikin yajin aiki a fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, shine ya bayyana hakan bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki na kungiyar a Abuja
Sanarwar tace in har suna shiga yajin aikin dole ne kamfanin man fetur na kasa NNPC ya dawo da tsohon farashin man fetur a kasar nan kafin su dakatar da zanga-zanga da yajin aikin na su