Shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPCL, Mele Kolo Kyari, ya shaida cewa za a dauki mataki a game da cire tallafin man fetur. A ranar Alhamis,
This Day ta ruwaito Mele Kolo Kyari ya na cewa Bola Tinubu ya yi umarni a samar da tsare-tsare da za su rage zafin janye tsarin.
Malam Mele Kyari ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen ‘yan jarida bayan zama da shugabannin jam’iyyar APC.
jaridar Leadership a jiya ta ruwaito Kyari na shaida cewa ba zai yiwu a ce kamfanin NNPCL ne kadai yake shigo da mai ba.
Za a bi sannu a hankali har ta kai ana bada kudin kasashen waje ga kowane mai bukatar su shiga kasashen Duniya domin su shigo da mai cikin Najeriya.
Kuma NNPC ba za ta cigaba da zama kamfani tilo da yake shigo da mai a kasar nan ba. Mun san za a kawo karshen wannan, kasuwar za ta mike da kan ta.”
Game da gyara matatun da ake da su, Kyari ya ce yanzu ana gyara wata matatar kuma zai fara aiki a shekarar nan, sauran za su dawo aiki a 2024 da 2025.
An kai matsayin da ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba za ta iya cigaba da biyan tallafn fetur ba, NNPCL GMD ya ce hakan ya jawo dole a cire shi.
A madadin hakan, sabon shugaban kasa ya yi umarni a samar da hanyoyin da za a ragewa talaka radadi a dalilin tashin da farashin man fetur ya yi a Najeriya.
“Ina da labari Mai girma shugaban kasa (Bola Tinubu) ya yi umarni a samar da wasu tsare-tsare da wasu shirye-shriye, kuma na tabbata za ayi hakan.”
Kyari bai yi bayanin irin abubuwan da za a fito da su a madadin tallafin fetur ba.
Sai dai yace Babu mamaki gwamnatin tarayya ta samar da motocin haya masu rahusa domin talakawa ko kuma ayi kokarin shigo da motocin da ba su amfani da fetur.