An bayyana cewa kudaden da masu rike da madafun iko na gwamnati shugaba Buhari suka wawashe a cikin shekaru 8 da suka gabata sun isa a raba wa kowane dan Najeriya Naira dubu 732.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Kwamishiniya a Hukumar kula da Harkokin Ƴan sanda ta Ƙasa, PSC, Najatu Mohammed, a wata tattaunawa ta musamman da gidan Radio Freedom, a wani bangare na bikin bayar da lambar yabo da lacca da aka gudanar kwanan nan don karrama wani jami’in dan sanda, Daniel Itse Amah.
Cibiyar Wayar da kan Al’umma kan Adalci da Amana, CAJA, ce ta shirya taron, tare da hadin gwiwar Cibiyar Penlight.
A cewar Najatu, idan har ba a shawo kan lamarin cin hanci ƙasar nan ba, nan da 2030 kowane dan kasa zai iya samun sama da Naira miliyan 1.4 idan za a dawo da kudaden da aka wawashe a raba.
Ta ce hanya daya tilo da kasar za ta iya gyara wannan ta’ada ita ce ta nuna wa jami’an gwamnati masu wawashe dukiyar talakawa kuskuren su da kuma kin zabar su.