Sojin sama sun kashe kwamandojin yan Boko Haram uku tare da mayakan su fiye da 100

Hedikwatar Rundunar sojojin saman kasar nan ta tabbatar da cewa jiragen yakinta sun kai wani mummunan farmaki akan gomman mayakan yan ta’addan Boko Haram inda ta hallaka wasu da dama.

A wata Sanarwar da Kakakin sojojin saman ya rabawa manema labarai ya ce an ga wasu gungun yan ta’adda sun tattaru a wani sansanonin dake Mantari bayan da wasu yan ta’adda suka zo cikin motocin yaki suna daf da kai hari.

Take kuma aka tada jiragen yaki inda suka afka musu a ka kuma sami nasarar hallaka manyan kwamandojin Boko haram uku da suka hada da Abba Tukur Maimusari da Bakura Jega

Kazalika bayan farmaki na farko da ya hallaka mayakan da dama daga bisani wasu mayakan sun dawo wannan sansanonin don debe gawawwakin mutanensu inda nanma jiragen yakin suka dawo suka kuma kara masu aman wuta. Kuma mayakan sama da Dari ne jiragen yakin suka hallaka.

Duka wannan kuma na zuwa ne a daidai Lokacin da manyan Hafsoshin kasa da na sama, Laftanar Janar Farouk Yahaya da Air Marshall Oladayo Amao ke ziyara a jihar Borno don yin Nikon kirsimati da dakarun dake bakin daga.

Kakakin sojojin saman yace Wani bayanin sittin da suka samu ya nuna yan ta’addan na shirin kai gari ne yayin da ake tsaka da bukukuwan kirsimati da na sabuwa shekara kana sun kuma tsara kawo cikas a babban zaben da za ai a shekara mai zuwa idan Allah ya kaimu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments