Yan sanda a kasar Uganda suna gudanar da bincike a kan wani turmutsitsi da ya faru ranar jajijibirin sabuwar shekara a birnin Kampala, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 9, ciki har da yara da dama.
Mummunan lamarin ya faru ne a wajen kasuwar zamani ta Freedom City Mall da ta shirya shagalin bikin sabuwar shekarar. A cewar ‘yan sanda, da tsakar dare mai gabatar da shirin bikin ya ce mahalartan su fita waje su yi kallon wasan wuta da ake yi.
“Bayan kammala wasan wutan ne aka samu turmutsitsin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar kana wasu da dama suka jikkata. Yayin da ma’aikatan agaji suka isa inda lamarin ya faru kuma suka kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutane tara suka mutu,” a cewar Lucas Owoyesigyire, mataimakin kakakin ‘yan sandan birnin Kampala.
Haji Kimera, da jikokinsa biyu suka mutu a wannan turmutsitsin, ya zanta da Muryar Amurka ta waya.
Ya ce a cikin yaran, daya ya samu nasarar zuwa aji bakwai makarantar sakandare yayin da dayan kuma ya shiga aji shida. Ya kara da cewa mahaifinsu ne ya kaisu wurin taron a Freedom Mall.
Kamar sauran kasashen duniya, miliyoyin ‘yan Uganda ne suka tarbi sabuwar shekarar 2023 da shagulgula, karon farko kenan aka yi bukukuwan tarbar sabuwar shekara bayan shekaru biyu saboda annobar COVID-19.