A yau 31/12/2022, dan takarar majalissar tarayya a kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jam’iyyar NNPP Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD,(Jarman Bebeji) ya gwanjage mutanen yankinsa da jari/tallafin kudade inda wasu suka rabauta da Dubu dari biyu(#200,000), Dubu dari daya(#100,000), Dubu Hamsin(#50,000), Dubu Ashirin(#20,000), Dubu Goma(#10,000) da kuma Dubu Biyar(#5,000).
Mutanen da suka amfana da wannan jari/tallafi sun hada da wakilan akwatuna, Exco na karamar hukuma da mazabu na Jam’iyyar NNPP da PDP na Kiru/Bebeji, KOKAS na Kiru/Bebeji, Wasu kungiyoyi masu karfi na mata da matasa a Kiru/Bebeji, Dagatan Kiru/Bebeji, Limaman Juma’a Kiru/Bebeji, Malaman Kwankwasiyya Kiru/Bebeji, Dalibai, Yan Social Media, Mafarauta, Yan Achaba, Mahauta da kuma mutane masu bukata ta musamman.
Wannan taro ya sami halartar yan takarkaru na Kiru/Bebeji, manyan jagorori tare da shuwagabannin jam’iyyar NNPP/PDP na Kiru/Bebeji.