Bayan shafe shekaru 20 a majalisar jihar Yobe Hon. Ahmed Lawan Mirwa ya taba kasa
Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Nguru dake jihar Yobe, Hon. Ahmed Lawan Mirwa na jam’iyar APC ya sha Kaye a hanun abokin karawar sa Musa Lawan Majakura na jam’iyar PDP.
Mirwa wanda shine shugaban zauren Majalisar jihar Yobe kafin yau ya shafe Zango Biyar ya lashe zabe a karamar Hukumar Nguru.
Jaridar Solacebase ta yanar gizo ta ruwaito cewa Musa Lawan Majakura ya lashe zaben da kuri’u 6,648 inda ya doke Ahmed Lawan Mirwa mai kuri’u 6,466 votes.