Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen jihar kano, tana ci gaba da kokawa akan rashin gurin tsayawa na din_din_din duk da gudunmawar da kungiyar take baiwa Gwamnati a fadin jihar nan.
Shugaban kungiyar Alh Abubakar Dan,iya Bala ne yake nuna koken nasu a wata zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Railway a nan jihar kano.
Shugaban ya bayyana cewa, Babban kalubalen da kungiyar take fuskanta bai wuce guri na din din din ba,Wanda kungiyar tana mutukar karshe makudan kudade wajen biyan kudin haya Wanda kuma, kamata yayi Gwamnati ce,za ta rika karbar wadan nan kudaden ko don ta yiwa al,ummar jihar kano aiki da su.
Yace, amma sakamakon haka,sai kungiyar take zuba kudaden a asusun yankasuwa dake da wurin ‘Ya’yan wannan kungiya za su tsaya domin gudanar da sana,arsu ta yau da kullum,kasancewar akasari mutane ne magidanta dake da nauyi a Kansu.
Abubakar Dan, iya Bala,yayi kira ga Gwamnatin jihar kano da ma’aikatar harkokin sufuri da gidajen ta jihar kano da sauran masu ruwa da tsaki,da su taimakawa kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa dake Railway, domin samun gurin da za ta rika ajiye motocin yankungiyarta.
Shugaban yace, wannan kungiyar ta Dade tana kiraye_kirayen Gwamnati ta tallafawa kungiyar, tun lokacin Gwamnatin da ta gabata,amma hakan ya ci tura,Wanda wannan lamarin abun dubawa ne.
Ya bayyana cewa, takwarorinta kungiyar na sauran jihohi suna mutukar sharbar roman dimakaradiyya,wadanda har mamaki suke yi idon kungiyar dake nan jihar kano tace,basu da gurin tsayawa na din din din da ‘ya’yanta za su rika tsayawa.
Shugaban ya jaddada kudirin Kungiyar na ci gaba da baiwa Gwamnatin cikakken hadin kan daya kamata domin ganin harkokin sufuri ya kara bunkasa yadda ya kamata a fadin jihar kano da ma kasa baki daya.
Haka zalika,ya yi kira ga’ya’yan kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen jihar kano dake railway, da su mayar da hankali wajen baiwa Gwamnati da kungiyar hadin kan daya kamata domin samun damar bijiro da managartan shirye_shirye da za su taimakawa wannan sana,a ta sufuri.
Daga karshe yayi kira ga yankungiyar, da su kaucewa tukin ganganci a lokutan da suke gudanar da ayyukansu na tuka motocin Akorikura.
Ibrahim sani gama pyramid radio.