Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya gudanar da nada-naden mukamin na farko a gwamnatin sa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Wadanda aka nada mukaman sun haɗa da:
1. Hon. Shehu Wada Sagagi, Shugaban Ma’aikata
2. Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jihar Kano
3. Dr. Farouq Kurawa
Babban Sakataren gwamnan wato PPS
4. Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, Shugaban tsare-tsare na gwamna
5. Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai
Sanarwar ta ce an zabi Wadannan nade-naden sun fara aiki ne daga yau Litinin 29 ga Mayu, 2023. Kuma an zabi wadanda aka nada ne bisa la’akari da tarihinsu, sadaukarwa da amincin su.