Gwamnan jihar Kano Engr Abba kabir Yusuf wanda aka fi Sani da Abba Gida-gida ya bayyana cewa zai dora tubalin gwamnatin sa akan ta tsohon gwamna sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kabir ya bayyana hakan ne jim kadan bayan karbar rantsuwa inda ya fita ran-gadi zuwa wasu maaikatu da makarantu mallakar gwamnatin jihar Kano
Gida-gida ya Sami ziyartar gurare da dama ciki harda makarantar kangararru dake karamar hukumar Kiru inda a take ya mayar da ita kyauta ga duk Wanda yaje karatu makarantar
Kazalika gwamnan yayi alkawarin dawo da aikin yashe kogin jakara tare da shimfida masa kwalta da fitilu kamar yadda sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kudurta.