Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da ke Hausawa filin Hockey a jihar Kano, a jiya Alhamis ta yanke wa shahararriyar jarumar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya, hukuncin sharar asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano har na tsawon makonni uku.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Murja ta shafe makonni uku a gidan yari bayan ƴan sanda sun cafke ta sun kuma gurfanar da ita a kotu.
Kotun dai na tuhumar Murja da laifuka da su ka shafi yarfe, ashariya, gurɓata tarbiyya da yunƙurin tada hankalin al’umma.
Hakazalika kotun, a makonni biyu da suka gabata, ta gurfanar da abokan Murja na TikTok su uku, da su ka haɗa da Aminu Ibrahim, mai lakabin BBC, Ashiru Idris Maiwushirya da kuma Sadiq Sharif, inda ta aike su gidan yari tare da ita.
Sai dai kuma da ya ke yanke hukunci a jiya, alƙalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Halliru ya yanke wa Murja hukuncin sharar makeken asibitin Murtala.
Sannan kuma za ta riƙa zuwa hukumar Hisbah ta jiha har tsawon watanni shida.
Haka suma, BBC, Maiwushirya da Sadiq Sharif, an yanke musu hukuncin sharar asibitin Murtala bisa kama su da laifin yaɗa batsa da yunkurin gurɓata tarbiyya, inda duk su ka amsa laifukan su.
Lauyan Zauren Malamai na jihar Kano, Badamasi Gandu, wanda su ne su ka shigar da korafi tun da fari, ya ce yanzu haka ana neman sauran ƴan TikTok ɗin irin su Ado Gwanja, Ummi Shakira da 442, wanda ya ke tsare a Nijar, inda ya ce su ma za a hukunta su idan an kama su.