Kotu ta tasa keyar Alasan Ado Doguwa zuwa gidan maza
Biyo Bayan zargin Dan majalisar tarayya dake wakiltar Tudunwada da Doguwa da rundunar yan sanda tayi na hada baki da wasu bata gari wajen kone wasu barayin Allah a ofishinsa jam’iyar NNPP na Tudunwada yanzu haka kotu ta tasa keyar Dan majalisar zuwa gidan maza.
Tun da fari da Ado ya shiga komar jamian yan sanda ne biyo Bayan kin amsa gayyatar da suka aike masa kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Huruna kiyawa.