Kungiyoyin matasa a arewacin kasar nan sun bayyana gamsuwarsu da yadda hukumar INEC ta gudanar da zaben 2023.
Kungiyoyin da suka hadar da na Sir Ahmadu Bello Youth Councile of Nigeria, da na Arewa Youth Council da kuma Advocate For Good Governance dukkaninsu sun yaba da yadda zaben na wannan shekara ta 2023 ya gudana.
A wani taron manema labarai da kungiyoyin na Arewacin kasar nan suka gudanar a dakin taro na Mumbayya dake Kano sun nemi alummar kasar nan dasu zama masu rungumar zaman lafiya a wannan lokaci na siyasa.
Amb Bilal Tijjani Faki shine shugaban kungiyar Sir Ahmadu Bello Youth Councile of Nigeria yace batun da wasu suke na cewar akwai magudi a zaben wannan shekara ba gaskiya bane.
Shima Zaidu Ayuba Alhaji shugaban kungiyar Arewa Youth Council yace sun tara dubban magoya bayane domin su nusar da alumma kan irin cigaban da aka samu a zaben na bana.
A nashi bangaran Ibrahim Munir Kankara yace taron nasu nada nufi nuna goyan baya ga cigaban dimukuradiyya da ma zaben na wannna lokaci.
Kiraye-kirayen na wadannan kungiyoyi na zuwane a daidai lokacin da wasu ke ganin hukumar zabe ta gaza aikewa da sakamakon zabe ta internet kamar yadda ta alkawarta.