Jam’iyyar PDP ta gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan shiga yaki da jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi har aka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki.
PDP ta ce kamata ya yi Tinubu ya watsar da irin wannan bakin tunanin, a maimakon haka ya shiga tattaunawa ta diflomasiyya don cimma nasarar da ake bukata, inji rahoton Daily Trust.
Kafar yada labarai ta Channels TV, tace Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed, ne ya bayyana hakan bayan wani taron jiga-jigan PDP da ya gudana a Abuja.
Gwamnan ya ce: “Gwamnonin sun shawarci shugaban kasa, babban kwamanda da gwamnatin tarayyar Najeriya da kada su shiga kowane irin yaki da Jamhuriyar Nijar kan juyin mulkin da soji suka yi a kasar.
Sun bukaci Tinibu yayi amfani da duk wani salo na tattaunawa da diflomasiyya.
Tun a baya,, Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya rubutawa majalisar dattawan Najeriya wasika game da matakin da kungiyar ta ke shirin dauka kan sojin Jamhuriyar Nijar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar dattawa wacce ke dauke da takunkumin da aka kakaba wa sojin na Nijar.