Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinta ta samu gagarumar nasara wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin ritayar tutoci 53 da aka gudanar na rundunar sojojin kasar.
Buhari ya bayyana irin dimbin kalubalen
tsaro da ya taras lokacin da ya amshi mulkin Najeriya shekaru takwas da suka gabata.
Yace nasarar ta hadar da murkushe mayakan Boko Haram, da ceto wadanda mayakan su ka yi garkuwa da su da dama, da kuma shawo kai da sake tsugunar da daruruwan mayaka da su ka ajiya makamai su ka mika wuya.
Buhari ya halarci bukin ritayar tutocin soji 53
Da yake tsokaci kan irin yadda aka tunkari matsalar tsaron tun farko, Shugaba Buhari yace, jim kadan bayan hawansa mulki, sun sami nasarar shawo kan matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa, yan aware, masu satar mai da sauran masu aikata manyan laifuka
Janar Buhari yace cikin shekaru takwas da yayi yana mulki, ya bada umarnin daukar zaratan sojoji sama da dubu sittin, banda dubban hafsoshin da kowacce shekara ake yayewa daga makarantar horas da hafsoshi ta kaduna
Dangane kuma da batun kayan aiki, Shugaba Buhari yace bayan irin hobbasan da yayi na samarwa sojojin daruruwan motocin sulke da harsasai basa iya ratsa su, da sauran kayayyakin aikin soji, an kuma sayi jiragen sama na aikin soji na zamani, tare da horas da jami’an sojin a fannin amfani da kuma kula da su