Hukumar lafiya ta duniya ta ce mayaka a kasar Sudan da ke fama da rikici sun mamaye dakin gwaje-gwaje na kasar, wanda ke dauke da samfuran cututtuka da suka hada da cutar shan inna da kyanda, lamarin da ka iya haifar da mummunar barazana ga lafiyar jama’a.
Mayakan sun kori dukkanin ma’aikatan daga dakin gwaje-gwaje wanda ya kasance a karkashin ikon daya daga cikin bangarorin da ke fada da juna, inda suka mayar da shi a matsayin sansanin soji, in ji Nima Saeed Abid, wakilin WHO a Sudan.
Sai dai bai bayyana ko wanne ne daga cikin bangarorin da ke fadan da juna bane suka kwace dakin gwaje-gwajen.
Abid ya ce ya samu kira daga shugaban dakin gwaje-gwaje na kasar da ke birnin Khartoum a ranar Litinin, kwana guda gabanin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta tsawon sa’o’i 72 tsakanin hafsoshin Sudan, bayan shafe kwanaki 10 ana gwabza fada a birane.
Daraktan dakin gwaje-gwajen ya kuma yi gargadin hadarin da ke tattare da wuraren jini na iya lalacewa saboda rashin wutar lantarki,” in ji Abid.
Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma tabbatar da cewa an kai hare-hare har sau 14 kan cibiyoyin kiwon lafiya a Sudan, inda aka kashe mutane takwas tare da jikkata wasu mutane biyu na daban.
Fadan da ake gwabzawa a kasar Sudan ya hada da dakarun da ke biyayya ga babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da na tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggawa ta musamman.