Shugaban sashen kulla yarjejeniya da doka na ma’aikatar kasuwanci a kasar China ya bayyana cewa, kasar sa za ta yi amfani da tsarin WTO na warware takaddama, game da matakan da Amurka ta dauka kan fitar da kayayyakin lantarki da sauran wasu kayayyaki zuwa kasashen Duniya.
Tuni kasar China ta Shigar da kara a gaban WTO, wanda ake ganin hakan wata hanya ce da ta dace don warware batutuwan ta hanyar doka, da kiyaye ‘yanci da ka’ida.
Jami’in na China ya ce, a cikin ‘yan shekarun nan, bangaren Amurka yana ci gaba da bayyana ra’ayin batun tsaron kasa, da yin amfani da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da kawo cikas a harkokin cinikayyar sassan lantarki na kasa da kasa, da sauran kayayyakin da aka saba bisa al’ada, da yin barazana ga zaman lafiyar tsarin samar da masana’antu a duniya, da kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da keta ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da keta muhimman ka’idojin tattalin arziki, da cutar da muradun zaman lafiya da ci gaban duniya, wanda hakan tamkar kariyar cinikayyar ce.