Wani Bayahude mai tsatsauran ra’ayi ya shiga wani cocin tarihi a tsohon birnin Gabashin Kudus da aka mamaye kuma ya kai hari kan gukin Annabi Isah da guduma.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da ‘yan sandan Isra’ila suka fitar, an bayyana cewa an kama dan yawon bude ido dan kasar Amurka da ya lalata gunkin a cocin da ke tsohon birnin.
Macid Rishik, jami’in tsaron cocin da ya tsayar da maharin ya ce maharin da ya taba haduwa da a yankin wani Bayahude ne mai tsatsauran ra’ayi.
Da aka tambaye shi ko me ya sa ‘yan sanda suka bayyana maharin a matsayin “Ba’amurke mai yawon bude ido” a cikin bayaninsa, Rishik ya sake nanata cewa “ya taba ganin wanda ya kai harin a yankin da cocin yake, kuma shi Bayahude ne mai tsatsauran ra’ayi.”
Da yake lura da cewa a da, Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi sun kai hare-hare kan coci kuma sun tayar da hankali, Rishik ya ce ya kai kara ga ‘yan sanda sau da yawa, amma an saki wadanda aka tsare kuma a koyaushe an rufe karar.
Friar Nikodemus Schnabel daga Cocin Latin na Katolika da ke Kudus a shafinsa na sada zumunta ya yi nuni da harin da aka kai wa cocin mai tsarki ga Kiristoci inda ya ce, “Barka da zuwa sabuwar Isra’ila, mai kyamar Kiristoci wacce gwamnati ke goya wa baya da karfafa wa gwiwa.”
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da rundunar tsaron birnin Kudus mai wakiltar al’ummar Kiristoci a Isra’ila ta fitar, an bayyana cewa karuwar laifuffukan da ake yi wa al’ummar Kiristoci kwanan nan ya tayar da damuwa kuma ana kira ga mahukuntan Isra’ila da su kare addinai marasa rinjaye.