Rikici akan limanci ya hana Sallar Juma’a a masallacin Juma’a na uku mafi girma a Kano

Cincirindon Jama’a sun yi dafifi suna tofin alatsine a masallacin Juma’a na uku mafi girma dake Unguwar kurnar Asabe a birnin kano.

Lamarin ya faru ne a jiya Juma’a sakamakon rashin lafiya da tayi tsanani ga babban limamin masallacin Sheikh Dan lami

Bayan tsanantar rashin lafiyar tasa ne Dan sa tare da wasu mukarraban sa suka ce Naibin masallacin bazai ja sallar Juma’a ba sai dai da ga babban limamin ne zai yi wa jama’a Sallar Juma’a.

Daga nan ne rikici ya barke har kimanin karfe uku da doriya jama’a basu samu sun yi Sallar Juma’a ba

A zantawar jaridar aksammedia da wasu daga cikin wadan da lamarin ya rutsa da su since hakan bayyi musu dadi ba Son zuciyar limamin ya hana su yin sallar Juma’a sai Azahar suka yi

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments