Tawagar masu sa ido a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya daga Tarayyar Turai, EU EOM ta bayyana damuwa game da nagartar zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.
A wani taro da ta gudanar a Abuja ranar Litinin, tawagar ta ce an saɓa doka game da sirranta takardar zaɓe a akasarin rumfunan zaɓe.
“Cikin rumfunan zaɓe 100 daga 240 da suka sa ido, hukumar ba ta tabbatar da sirranta ƙuri’u ba sannan fiye da rabin masu kaɗa kuri’ar ba su sirranta takardar jefa ƙuri’a ba,” kamar yadda tawagar ta faɗa a rahotonta.
A cewarta, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nuna takardar kaɗa ƙuri’arsa domin nuna jam’iyyar da ya zaɓa a ranar zaɓen.
Yayin da take magana game da tangarɗar da aka fuskanta da na’urar BVAS a wasu rumfunan zaɓe, tawagar ta kuma ce ba a bi muhimman ƙa’idojin da aka gindaya ba a tsarin zaɓen.
“A rumfunan zaɓe 32 da aka sa ido, ba a yin wata alama a jikin rajistar sunayen masu zaɓe. Masu sa ido sun bayyana cewa an samu ƙananan yara da suka yi zaɓe a Sokoto da Kano. “Ta ce gabanin zaɓen, masu ruwa da tsaki sun bayyana gamsuwa da ƙwarewa da ƙoƙarin hukumar zaɓe mai zaman kanta na wayar da kan masu zaɓe amma an rasa duka waɗan nan yayin da ranar zaɓe ke gabatowa a Kano da Legas.
“A daren ranar zaɓen, an ga yadda aka riƙa fidda rai game da tsarin hukumar zaɓen, saboda giɓin da aka riƙa samu wajen fitar da bayanai da kuma gazawar INEC ta yin wani abu game da damuwar da masu ruwa da tsaki suka nuna kan matsalolin tsaro da isar kayan aiki rumfunan zaɓe da kuma rashin ɗora sakamakon zaɓen a shafinta na intanet.
Yayin da ta tabbatar da cewa hukumar zaɓen ta yi ƙoƙari wajen bayyana sakamako a bainar jama’a , tawagar ta EU EOM ta ce akwai naƙasu a yadda aka gudanar da tsarin zaɓen a wurare 9 cikin 37 da aka sa ido.
“Tawagar ta ga yadda aka samu rashin ba da muhimmanci ga tsare-tsaren cike foma-fomai da kuma killace muhimman kayan aikin zaɓe. A rumfunan zaɓe 16 cikin 37 da aka sa ido, ma’aikata sun fuskanci ƙalubale game da yadda za su cike takardar sakamakon zaɓe. Ta ce an samu saɓanin alƙaluma a wasu rumfunan zaɓen da tawagar ta sa ido.
Ta kuma yi ƙorafin yadda aka gaza ɗora sakamakon zaɓen a shafin hukumar ta hanyar amfani da BVAS.