Bayan shafe shekaru 16 yana sanatan Kano ta kudu, Kabiru Ibrahim Gaya ya sha Kaye a hannun Kawu Sumaila

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan kano ta kudu.
Farfesa Ibrahim Barde babban Baturen zaɓe na shiyyar Kano ta kudu shi ne ya bayyana da hakan ga manema labarai a garin Rano.
A cewar sa kawu Sumaila  ya Sami kuri’u mafi rinjaye Kuma ya cika dukkanin ka’idoji da hukumar zabe mai zaman kanta  ta tanada don haka shi ne ya lashe wannan zabe na Sanatan kano ta kudu.
Kawu Sumaila ya samu kuri’u 319,557 yayin da babban abokin karawar sa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na jam’iyyar APC ya sami kuri’u 192,518, wanda hakan ya nuna Kawu Sumaila a matsayin wanda  ya sami kuri’u mafi rinjaye
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments