Mataimakin kakakin Majalisar dokokin Kano ya fice daga APCMataimakin Shugaban majalisar Jihar Kano Hon. Zubairu Hamza Massu ya Sanar da ficewarsa daga Jama’iyyar APC a yau Alhamis.
Wakilin Aksammedia ya rawaito Dan Majalisar wanda shi ke Wakiltar Karamar Hukumar Sumaila a Majalisar dokokin Jihar Kano ya bayyana ficewar tasa ne cikin wata wasika Mai kwanan watan 12 ga watan mayu 2022, da ya aikewa Shugaban jam’iyyar APC na mazabar da ta Massu .
A cikin Wasikar Hon. Hamza Massu bai bayyana Sabuwar jam’iyyar da ya Koma ba, Amma dai ana hasashen jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari ta Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hon Massu dai Suna da kyakykyawar alaka da Hon. Abdulrahman kawu Sumaila Wanda ya shi aka ce yana daf da aiyana ficewarsa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP Mai kayan marmari.