Dan takarar Gwamna a jamiyyar PRP Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta Kai ziyara daukacin mazabun jiharnan domin sanin halin da suke ciki.
Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Dan takarar ya bayyana cewar shi kadai ne Dan takarar da ya iya zagayawa kananan hukumomin jiharnan 44 domin sadar da zumunci da kuma neman tubarraki ga limamai da sarakunan gargajiya tun da aka kada gangar siyasa a fadin jihar Kano.
Yakasai ya kuma bayyana cewar ya fara siyasa ne tun sama da shekaru Ashirin baya kuma da zarar an fara gangamin zabe zaa ga salon siyasa Wanda ake yiwa lakabi da Namu-ba-irin-Nasu-bane kasancewarsa a matsayin wanda ya fara siyasa tun daga tushe.
Ya kara da cewar yanzu haka shirye shirye sun kammala wajen ziyarar mazabun daukacin jiharnan 484 domin sanin halin da suke ciki wanda yace wannan shima salo ne da babu wata jamiyya da zata jure hakan a fadin jihar nan.
Kazalika Yakasai ya bayyana kadan daga cikin tarihin rayuwarsa wanda yace hakan na nuni cewar shi ba sabon shiga bane a harkokin mulki, inda ya zayyana cewar yayi aiki da gwamnatin Dakta Abdullahi umar Ganguje a matsayin mai bashi shawara kan harkokin yada labarai,yayi kuma yi Daraakta janar media a gwamnatin jihar Kano, yayi aikin jarida da gidan rediyon freedom, kana kuma ya kwashe sama da shekaru Ashirin yana tsayawa takara daban daban wanda hakan ta sanya ya zama kwararren dan siyasa mai burin ya taimaki alummar jiharnan musamman talakawa.
Alhaji Salihu ya bayyana cewar salon da wannan siyasa ta yanzu ta zo dashi salone da ba a taba yin irin sa ba tun da aka fara demokaradiyya a fadin kasarnan kasancewar dogon zango da salon yake dashi wanda a baya daga yin zaben fidda gwani cikin wata daya ko biyu sai kaga an fara gangamin zabe sai kuma babban zabe wanda yanzu bayan anyi zaben fidda gwani sai an dauki dogon lokaci kafin a fara gangamin zabe, Sannan daga nan Sai an kwashe watanni biyar zuwa shida kafin a gudanar da babban zabe.
Don haka yace wannan salon wata dama ce da suka samu domin zagayawa wajen wayar da kan alumma da kuma tabbatar da ganin an zabi nagartattun mutane ba masu son zuciya ba.
Daga karshe ya jajantawa alummar jiharnan musamman wadanda ibtilain ambaliyar ruwa ta Shafa a wasu kasuwannin jiharnan da kuma ibtilain rugujewar gini a kasuwar wayoyin hannu dake Berut tare da fatan Allah ya kare aukuwar hakan anan gaba.