Shugaban cibiyar hada magunguna na kasa Dr.mamman ya fara da godewa Allah bisa ganin wannan sabuwar shekara ta 1444 ya taya daukacin Al’ummar musulmai farin cikin ganin wannan shekara
Daga wakilin aksammedia B.imam
Ya kara da tinasar da al’umma wajan godewa Allah kamar yadda shugaban halitta ya koyar da sahabban sa masu daraja dasu kasance masu godewa Allah saw a duk lokacin da suka riski kansu a sabuwar shekara.
Sannan yaja hankalin al’umma dasu raya sunnar azimi na 9 da 10 ga wata da yaga yahudawa keyi sabida annabi musa inda shima ya daura niyyar in Allah yasa yakai wata shekarar zaiyi azimin 9 da 10 ga wata
- Daga karshe yayi addu’ar game da matsalolin da suka addabi Al’ummar wannan kasa da kuma fatan samun sabbin shuwagabannin na gari