An yi zanga-zanga kan yawan kisan jakuna a Najeriya.
Daga Walid Hari.
Ɗaruruwan mutane ne a Najeriya suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda ƴan China ke yanka jakuna ba bisa ƙa’ida ba a ƙasar.
Mutanen na zargin ana ci gaba da kashe jakunan duk da umurnin da gwamnati ta bayar na dakatar da hakan.
Sun kuma zargi ministan harkokin noma da yin sakaci, ta hanyar barin mutane daga ƙasar waje suna gudanar da cinikayyar sassan jikin jakunan.
Yanzu haka dai akwai wani ƙuduri a majalisar dokokin ƙasar na neman a sanya ido kan yadda ake cinikayyar jakunan.
A watan jiya hukumar hana-fasa-kwauri ta Najeriya ta kama mazakutar jaki guda 7,000 a filin jirgin sama na Lagos, waɗanda ake ƙokarin fitar da su zuwa China.