An gano yadda Tinibu ya yi amfani da Obi wajen bawa Atiku matsala a lokacin zabe

Tinubu Ya Yi Amfani da Obi, Ya Hana Atiku Samun Mulki Inji ‘Dan Takaran LP

Tawfiq Akinwale ya fito yana ikirarin Bola Ahmed Tinubu ya roki Pat Utomi ya janye takararsa Farfesan ya samu tikitin Jam’iyyar LP, amma ya sallama takararsa ga Peter Obi da ya zo na uku a 2023

‘Dan takaran LP a zaben Gwamnan Oyo ya ce Tinubu ya taimakawa takarar Obi a Jam’iyyar adawar

  Tawfiq Akinwale wanda ya yi wa jam’iyyar LP takarar Gwamna a jihar Oyo ya bayyana abin da ya faru a zaben 2023 ta bayan fage. Da aka yi hira da shi a gidan rediyon YES FM a garin Ibadan,

Tawfiq Akinwale ya ce Asiwaji Bola Tinubu ne ya roki Pat Utomi ya hakura da takara. Zababben shugaban kasar ya shawo kan Farfesa Utomi, ya bar Peter Obi ya nemi kujerar shugaban kasa a madadinsa a jam’iyyar LP mai adawa.

‘Dan takaran Gwamnan ya kara da cewa har Utomi ya samu takarar shugaban kasa, amma da Tinubu ya lallabe shi, sai ya kyale Obi ya rike tutar jam’iyyar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments