Ga dukkan alamun za a naɗa tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC ranar Alhamis
Ana tsammanin hakan zata faru ne a wurin taron majalisar zartarwa (NEC) wanda APC ta tsara gudanarwa ranar 3 ga watan Agusta
Tuni shugaba Tinubu ya faɗa wa Ganduje shirinsa na maida shi shugaban APC don haka ya cire sunansa daga Ministoci
Tun fari APC ta tsara gudanar da waɗannan tarukan biyu a watan Yuli amma hakan bai yuwuwa ba sakamakon murabus ɗin tsohon shugaba, Abdullahi Adamu da sakatare, Iyiola Omisore.