Ranar Litinin ne gwamnatin tarayyar Nigeria, za ta gana da wakilan kungiyoyin kwadago a kokarinta na dakile yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasar ta kira a fadin kasar.
Mataimakin babban sakataren kungiyar ta NLC, Chris Onyeka, ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da manema labarai , inda yace suma ‘yan kasar su rage yawan zirga-zirgar su domin gudun kada su fuskanci matsala.
Kuma kungiyar NLC ta shawarci ‘yan Nigeria da su tanadi kayan abinci da magunguna da sauran muhimman abubuwan bukata na yau da kullum a gidajensu, gabanin fara yajin aikin na kwanaki bakwai domin nuna adawa da cire tallafin man fetur da kuma tsadar rayuwa da ake fama da ita a Nigeria.
“Gargadin ya zama dole ne saboda yajin aikin zai tsayar da komai a kasar, duba da za a takaita zirga-zirga sosai yayin da wuraren kasuwanci da makarantu da wuraren kiwon lafiya za su kasance dukkaninsu a kulle.
Jaridar kadaura24 ta rawaito cewa NLC ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki bakwai tare da barazanar fara yajin aikin gama gari a fadin Nigeria a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023.
Kungiyar a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Joe Ajaero, ta zargi Gwamnatin tarayya da gaza biyan bukatun da ta gabatar mata biyo bayan cire tallafin mai, wanda ya haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi a Nigeria.
Biyo bayan sanarwar yajin aikin da kungiyar kwadago ta yi, nan take tawagar gwamnati ta kira taron gaggawa da kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar kwadago ta NLC a ranar Juma’ar da ta gabata a fadar Gwamnatin tarayya.
Sai dai jami’an kungiyar da suka hada da kungiyar sun fice daga taron a fusace sakamakon gazawar da tawagar gwamnati ta yi.
Onyeka ya bayyana cewa kungiyar kwadagon za ta gana da gwamnati ranar litinin, inda ya kara da cewa sakamakon taron zai tabbatar da mataki na gaba.
Ya ce, “Ya kamata ‘yan Najeriya su shirya. Abin da muke cewa ke nan. Kasancewa cikin shiri yana nufin dole ne ku tanadi abinci a cikin gidan ku don gudun fadawa cikin kalubale