Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce yan Najeriya za su ga kyakkyawan sauyi nan da wata tara ko shekara ɗaya karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin hakan ne a jiya Juma’a a birnin St Petersburg yayin wani zama da yan Najeriya mazauna kasar Rasha.
Kashim ya tabbatarwa ƴan Najeriya musamman ma waɗanda ke zaune a ƙasar Rasha, cewa gwamnatin Tinubu za ta yi aiki tukuru don kawo ci gaba.
A lokacin da yake tattaunawa da ƴan Najeriyar, Kashim ya ce “ina tabbatar muku cewa nan da wata tara zuwa shekara ɗaya, za a samu sauyi mai kyau a Najeriya, na faɗi haka ne saboda na yi imani da irin hazakar da Shugaba Bola Tinubu ke da shi.”
Ya ce gwamnati mai ci na yin duk ƙoƙarinta wajen kyautata yanayin tattalin arzikin ƙasar da kuma farafad da kamfanoni da za su kawo mata ci gaba.
Shettima ya kuma suna da burin horas da ƴan Najeriya miliyan ɗaya a ɓangaren ilimin zamani na intanet.