A kalla yara sama da 60 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar amfani da wani magani

An fitar da wani gargaɗi na duniya kan wasu nau’ukan maganin tari huɗu bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargaɗin cewa wataƙila suna da alaƙa da mutuwar yara 66 a ƙasar Gambiya.

An ce akwai yiwuwar magungunan na da alaƙa da jawo mummunan ciwon ƙoda da kuma kisa ga yara.

Wani kamfanin ƙasar Indiya Maiden Pharmaceuticals ne, ya samar da magungunan, kuma ya gaza tabbatar da ingancinsa, kamar yadda WHO ta ƙara da cewa.

Har yanzu kamfanin bai ce komai ba
BBC ta tuntuɓi kamfanin Maiden Pharmaceuticals don jin ta bakinsa.

WHO ta ce magungunan su ne Promethazine Oral Solution da Kofexmalin Baby Cough Syrup da Makoff Baby Cough Syrup da kuma Magrip N Cold Syrup.

An gano dukkan magungunan ne a Gambiya, amma kuma ana samun su a wasu kasuwannin a wasu ƙasashen da ke yankin Afirka ta Yamma”, in ji WHO, a wata maƙala da ta wallafa a shafinta na intanet.

WHO ta yi gargaɗin cewa amfani da magungunan na iya janyo mummunan ciwo ko mutuwa, musamman a tsakanin yara.

WHo ta shiga cikin lamarin ne bayan da hukumomin lafiya a Gambiya – ƙasar da ta yi fice kan harkar buɗe ido – ta gano yadda ake samun ƙaruwar ciwon ƙoda a tsakanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar tun daga watan Yuli.

Tuni gwamnatin Gambiya ta dakatar da amfani da duk wani maganin ruwa na paracetamol ta kuma nemi mutane da su yi amfani da ƙwayar maganin maimakon na ruwan.

WHO ta ce sakamakon gwajin da aka yi a kan magungunan sun nuna cewa suna ɗauke da sinadaran da ba a yarda da su ba na diethylene glycol da ethylene glycol.

“Sinadaran na da guba, kuma illarsu “ka iya haɗawa da ciwon ciki da amai da gudawa da rashin yin fitsari da ciwon kai da taɓa lafiyar hankali da kuma jawo mummunar ciwon ƙoda da ka iya jawo mutuwa”, ya ƙara da cewa.

Jami’an lafiya na Gambiya sun ce a watan da ya gabata gwamman yara ne suka mutu ba tare da sun fadi ainihin yawansu ba.

Da yake magana a Geneva a ranar Laraba, shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce: “Mutuwar waɗannan yara abu ne mai karya zuciyar ga iyalansu.”

WHO ta ce hukumar kula da ingancin magunguna ta Indiya ta gano cewa wataƙila a Gambiya ne kawai kamfanin ya samar da magungunan, kamar yadda AFP ta ruwaito, tana mai ambato hukumar lafiyar MDD.

Amma WHO ta ce “akwai yiwuwar ya bazu a duniya don wataƙila kamfanin ya yi amfani da sinadaran masu illa wajen yin wasu magungunan a Indiya ko fitar da su wasu

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce mutuwra yaran abin tausayi ne

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments